A ranar Lahadi, an kama 'yan ci rani takwas a garin Illizi da kuma uku a garin Adrar, wato a kudu maso gabashi da kuma kudu maso yammacin kasar. A jajibirin wannan rana, wasu 'yan ci rani 49 da ke zama a kasar ba bisa doka ba, da suka fito daga wasu kasashen Afrika daban daban da kuma aka cafke a garuruwan Tamanrasset, In Guezam da Bordj Badji Mokhtar dake kan iyakoki da kasashen Nijar da Mali. (Maman Ada)