in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta fara zagayen karshe na rajistar masu zabe miliyan 6
2017-01-16 10:51:07 cri
Hukumar zaben kasar Kenya ta ce ta fara zagayen karshe na aikin rajistar masu zabe wanda take burin yiwa mutane miliyan 6 rajistar.

Babban daraktan zartaswar hukumar zabe da shata kan iyakoki mai zaman kanta IEBC, Ezra Chiloba ya shedawa 'yan jaridu a birnin Nairobi na kasar cewa, ya zuwa watan Disambar shekarar 2016, hukumar ta yiwa mutanen Kenya miliyan 15.9 rajistar, kana IEBC ta tantancesu.

Chiloba ya fada cewa, an fara gudanar da zagayen karshe na rajistar masu zaben ne tun daga yau Litinin, kuma ana saran za'a yiwa sabbin masu kada kuri'a miliyan 4 zuwa miliyan 6 rajistar.

Hukumar din ta IEBC ta fara aikin rajistar masu zaben ne na kwanaki 30 wanda aka fara daga ranar 16 ga watan Janairu zuwa 14 ga watan Fabrairu.

Wannan shi ne zagayen karshe na rajistar masu zaben, kafin gudanar da babban zaben kasar a ranar 8 ga watan Augasta.

Chiloba ya ce kundin tsarin mulkin kasar ya baiwa duk 'yan kasar ta Kenya damar shiga a dama da su a harkokin siyasa. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China