in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AFDB zai dauki nauyin aikin samar da wutan lantarki a kasar Kenya
2017-01-06 10:20:26 cri
A jiya Alhamis ne asusun samar da makamashi mai tsafta a nahiyar Afirka wanda ke karkashin kulawar bankin raya Afirka(AFDB) ya amince ya samar da rancen dala 992,000 ga aikin samar da wutan lantarki ta hanyar amfani da ruwa mai karfin megawatts 7.8 a kasar Kenya.

Bankin na AFDB ya ce,idan aikin ya kammala, zai taimaka wajen bunkasa manufar kasar Kenya ta kara fadada hanyoyinta na samar da wutan lantarki a kasar.

Babban darektan ofishin banki mai kula da harkokin kasuwanci da raya yankunan gabashin Afirka, Gabriel Negatu ya ce, aikin zai kuma samar da guraben ayyukan yi da hanyoyin kudaden shiga, musamman ma ga mata.

A nasa bangaren shugaban kamfanin samar da wutan lantarki mai kula da yankin Mutunguru, Patrick Kimathi, ya bayyana cewa,gwamnati tana daukar kananan tashoshin samar da wutan lantarki ta hanyar amfani da karfin ruwa da muhimmanci matuka, bisa la'akari da makuden kudaden da ake kashewa, kayayyakin da ake amfani da su da kuma saukin sarrafa tashar.

Kimathi ya ce, da zarar an horas da al'ummomin yankunan karkara yadda za su kula da kuma cin gajiyar kananan tashoshin samar da hasken wutan lantarkin masu amfani da karfin ruwa da ke yankunan nasu, gwamnati a nata bangare za ta rika karbar kudin wutan da suke amfani da su, a wani mataki na kara samar da makamashi mai dorewa ,tsafta da kuma rahusa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China