in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An harbe wani mutum a wani tashin hankalin yan wasan kwallon kafa a Brazil
2017-02-15 16:56:11 cri
A ranar Lahadin data gabatane aka harbe wani mutum har lahira kana wasu mutanen 7 suka samu raunuka a lokacin tashin hankali tsakanin magoya bayan kungiyoyin wasannin kwallon kafa a Rio de de Janeiro na kasar Brazil.

Diego Silva dos Santos, mai shekaru 28, an hallakashine a wajen filin wasan Rio Olympic, a lokacin da tarzoma ta barke tsakanin magoya bayan kungiyoyin wasannin na Flamengo da Botafogo.

Jami'an kungiyar wasan Botafogo sun nuna damuwa tun kafin gudanar da wasan game da samar da tsaro a lokacin da ake fuskantar harbe harbe daga wasu jami'an yan sandan Rio.

Mai magana da yawun yan sanda ya musanta zargin da ake yi musu na kaddamar da harbe harben a filin wasan.

Kungiyar wasan Flamengo ta lallasa Carioca da ci 2-1 a wasan cin kofin kwararru. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China