Yayin wasan na karshen mako da ya gabata dai Barca ta je har gidan Deportivo Alaves, ta kuma lallasa ta da ci 6 da nema.
Shafin yanar gizo na Barcelona ya tabbatar da cewa Alaves ya hada kafa da mai tsaron bayan Deportivo Theo Hernandez, kuma kyamarorin filin wasan sun nuna yadda ya gurde kafar ta sa a wannan lokaci, nan take kuma ya bukaci da a kawo masa dauki.
Masu lura da lafiyar 'yan wasa sun fitar da shi daga fili, kafin kuma a garzaya da shi asibiti.
Da yake tsokaci game da aukuwar hakan, dan wasan da suka hada kafa da shi Theo Hernandez, ya ce "na kai kafa domin dauke kwallo yayin da ya kai ta shi kafar sai muka yi karo, wannan lamari tsautsayi ne, ina fatan zai samu sauki cikin hanzari. Gaskiya abun takaici ne a duk lokacin da ka yi sanadiyyar jikkatar abokin wasan ka, ina fatan zai yafe min.(Saminu Alhassan)