in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamaru ta gudanar da baje-koli mafi girma a tsakiyar Africa
2017-02-15 10:13:14 cri
Jamhuriyar Kamaru ta gudanar da bikin baje-koli na kasa da kasa karo 6, mai taken PROMOTE 2017 wanda aka gudanar a Yaounde babban birnin kasar.

Firaministan kasar Philemon Yang, shi ne ya jagoranci kaddamar da bikin baje-kolin a ranar Litinin din data gabata, kuma ya samu halartar 'yan kallo na cikin gida da ma kasashen ketare.

PROMOTE shi ne baje-koli mafi shahara da aka taba gudanarwa a tsakiyar Afrika. Tun bayan wanda aka gudanar a karon farko a shekarar 2002 a Yaounde, wanda a wancan lokacin kamfanonin shiyyar tsakiyar Afrika ne kadai suka halarci bikin. Amma a bikin wannan shekara sama da kamfanoni 1,300 daga sassan duniya dabam dabam ne suka halarci bikin, kuma daga cikin wannan adadin, kamafanoni 1,000 sun fito ne daga yankin tsakiyar Afrika, kana ragowar kuma daga sauran sassa na duniya.

Wanda ya shirya baje-kolin na PROMOTE 2017 ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Talata cewa, mafi yawan kamfanonin da suka halarci baje-kolin kanana da matsakaitan kamfanoni ne wadanda suke da muradin tallata kamfanoninsu da kuma kulla dangantaka da sauran abokan hulda.Wata 'yar kasuwa dake saka jakakkunan da hulunan mata daga kasar Madagascar, ta shedawa Xinhua cewa, wannan shi ne bikin baje-koli mafi girma a nahiyar Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China