Wadannan jami'ai 4 da suka hada da William Swing, babban darektan hukumar kula da batun 'yan ci rani, da Filippo Grandi, babban kwamishina mai kula da batun 'yan gudun hijira, da Zeid Al Hussein, babban jami'i mai kula da batun kare hakkin dan Adam, gami da Martin Kobler, manzon musamman na babban sakataren MDD kan batun Libya, sun gudanar da taro a jiya Jumma'a a birnin Geneva, inda suka tattauna kan matakan da za a iya dauka don daidaita matsalar kwararar 'yan gudun hijira.
Jami'an 4 sun kara da cewa, a kan kama 'yan gudun hijira da suka tsaya a kasar Libya ba tare da bin matakan shari'a ba, kuma yanayin gidajen kaso da ake tsare wadannan mutane ba shi da inganci ko kadan, lamarin da ya sa mutanen ke fama da tamowa, da azaba iri-iri.
Al'amarin da ya sa jami'an ke kira ga kasashen duniya su mai da hankali kan batun.(Bello Wang)