Da fari dai Swansea ne suka mamaye wasan gabanin hutun rabin lokaci, kafin Manchester city ta sauya salon wasan bayan dawowa daga hutu. Wasan dai ya sanya Manchester city darewa matsayi na 3 a teburin gasar ta Firmiya.
A daya bangaren kuwa, mai rike da kambin gasar Leicester city, ta yi kasa matuka, inda a yanzu haka maki daya ya rage mata ta fada wajen gasar, bayan da wasan ta na baya bayan nan Manchester United ta bita har gida ta jefa mata kwallaye 2 cikin mintuna 2. Henrikh Mkhitaryan ne dai ya ciwa Manchester United kwallon farko. Sai kuma kwallon Zlatan Ibrahimovic.
Leicester sun rasa dukkanin wani kuzari na zura kwallo a raga tun ma kafin a tafi hutun rabin lokaci, yayin da Manchester United ta ci gaba da kaddamar da hare hare. Yanzu haka dai Manchester United din ce ke matsayi na 6 a teburin gasar ta Firimiya, inda Liverpool ke gaban ta da maki daya, yayin da Arsenal ta wuce gaban ta da maki 2 a matsayi na 4.(Saminu Alhassan)