in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barca Sevilla sun matsa saman teburin La liga bayan da Real Madrid ta yi kwantan wasa
2017-02-08 16:57:55 cri
A ci gaba da buga gasar kwallon kafar La Liga ta Sifaniya, wasannin mako na 21, Barcelona ta lallasa Athletic Bilbao da 3 da nema a gida, sakamakon rawar gani da Leo Messi da Neymar suka taka a wasan, yayin da a daya hannun masu nazarin wasan ke ganin Golan Bilbao Gorka Iraizoz, shi ma ya gaza matuka wajen dakatar da kwallayen Barcelona.

Paco Alcacer ne dai ya fara zura kwallon farko a ragar Bilbao cikin mintina 17. Sai kuma kwallon Leo Messi ta bugun free kick. Yayin da kuma Aleix Vidal ya kammala cin kwallayen ga Barca.

A daya bangaren kuma Sevilla sun tashi kunne doki maras ci da Villarreal. Mai tsaron gidan Villarreal Sergio Asenjo ya tare kwallon bugun daga kai sai mai tsaron gida wadda Samir Nasri ya buga, haka kuma ya ture kwallayen Wassim Ben Yedder da ta Vicente Iborra.

A wasan Atletico Madrid da Levante, Fernando Torres ya ciwa kungiyar Atletico kwallo daya tilo tun cikin watan Satumba, mintuna 15 da take wasa.

Ita ma Espanyol ta samu nasara kan Malaga da ci daya da nema, ta hannun dan wasan ta Pablo Piatti. Malaga dai ta buga wasanni 8 ba nasara bayan wasan ta na karshen mako.

Sauran wasannin makon na 21 dai sun hada da wasan da Sporting Gijon ta lassasa Alves da 4 da 2. Real Sociedad ita ma nasara ta yi a wasan ta da Osasuna, inda suka tashi 3-2. Sai kuma kungiyar Eibar wadda ta yiwa Valencia dukan kawo wuka da ci 4-0.

Rashin kyawun yanayi, na mamakon ruwa da iska mai karfi sun lalata wani sashi na rufin filayen wasannin Riazor da Balaidos. Wanda hakan ya sanya dage wasan Deportivo la Coruna da Betis, da kuma wasan da Celta Vigo ya dace ta bugu da Real Madrid.

Yanzu dai Real Madrid ce a saman teburin La Liga da maki 46, sai Barcelona ta 2 da maki 45. Sevilla ce ta 3 da maki 43, yayin da Atletico Madrid da Real Sociedad ke matsayi na 4 da na 5.

Can kasan teburin kuwa Granada na matsayi na 19 da maki 13, yayin da kuma Osasuna ke na 20 da maki 10.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China