Dan wasan Lobi Kingsley Eduwo ne dai ya zura kwallon farko a ragar Wakki cikin mintuna 52 da take wasa, kafin kuma Kwambe na Wikkin ya jefa kwallo ta biyu ta bugun daga kai sai mai tsaron gida.
A birnin Akure kuwa, dan wasan MFM FC Stephen Odey ne ya ci wa kungiyar sa kwallo ta 5 a kakar bana, a wasan da suka buga da kungiyar Sunshine Stars a filin wasa na birnin Akure. An dai tashi wasan MFM na da kwallo daya Sunshine na nema. Kawo yanzu dai ba a samu nasara kan 'yan wasan na MFM ba a wasanni 4 da suka buga a gasar ta NPFL ta bana, ita ce kuma kungiyar dake matsayi na 2 a teburin gasar da maki 13.
A matsayi na farko kuwa Plateau United ce, wadda ke ci gaba da rike damar buga wasanni ba tare da an samu nasara a kan ta ba. A baya bayan nan ma dai ta tashi kunnen doki maras ci tare da kungiyar Nasarawa United a wasan su na birnin Lafiyar jahar Nassarawa.(Saminu Alhassan)