in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta dakatar da matakin hana 'yan gudun hijira shiga kasar
2017-02-05 13:12:09 cri
Wani alkali a kotun dake yankin yammacin jihar Washington ta kasar Amurka James Robart, ya yanke hukunci a Jumma'a da ta gabata cewa, an dakatar da aiwatar da matakin hana 'yan gudun hijira shiga kasar wanda shugaban kasar Donald Trump ya kayyade cikin wani umarnin da ya bayar. Daga bisani a jiya Asabar, ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da dakatar da umarnin da shugaba Trump ya yi na takaita shigar 'yan kasashen waje cikin kasar ta Amurka.

Cikin sanarwar da ta gabatar, ma'aikatar tsaron Amurka ta ce an dakatar da matakin ne bisa hukuncin da alkalin kotun ya yanke, don haka za a maido da tsarin da ake bi a baya a fannin binciken 'yan kasashen waje masu neman shiga kasar Amurka.

Wasu kafofin watsa labaru na Amurkar sun sheda cewa, bayan da Alkali Robart ya yanke hukuncin ne, hukumomin kwastam da na shigi da fici na kasar suka sanar da manyan kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama da su maido da tsarin da suke bi a baya. Daga baya kuma, a ranar Asabar, an fara baiwa fasinjoji da umarnin shugaba Trump ya shafa damar shiga kasar Amurkar.

Ban da haka kuma, a yammacin ranar Asabar da ta gabata, bisa agogon wurin, dubban jama'ar kasar Amurka sun yi gangami a dab da fadar White House, wato fadar shugabancin kasar Amurka, inda suka yi zanga-zangar kin amincewa da umarnin da shugaba Donald Trump ya bayar na takaita shiga cikin kasar. Hakan ya kasance karo na 2 a jere da aka gudanar da zanga-zanga don nuna kin yarda da umarnin, zanga-zangar da ta gudana a karshen mako. Har ila yau, a birnin New York da jihar Florida na kasar, jama'a da dama sun yi zanga-zangar tir da umarnin shugaba Donald Trump na takaita shiga kasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China