Umarnin da shugaban ya gabatar a ranar 27 ga watan Janairu ya hana 'yan gudun hijira da wasu 'yan kasashe 7 a yammacin Asiya da arewacin Afirka shiga kasar ta Amurka. Wannan ya nuna cewa, Amurkar ba za ta karbi 'yan gudun hijira ba cikin kwanaki 120, kana an hana 'yan kasashen Iran, Sudan, Syria, Libiya, Somaliya, Yemen, da Iraki shiga kasar cikin kwanaki 90, haka kuma an hana 'yan gudun hijira na kasar Syria shiga cikin kasar Amurka ba tare da sanya wani wa'adi ba.
Bayan da shugaba Trump ya ba da wannan umarnin, Amurkawa suke ta sukarsa, tare da gudanar da zanga-zangar kin amincewa da wannan mataki, sa'an nan wasu kasashe da dama su ma sun bayyana ra'ayinsu game da kin yarda da wannan mataki na Trump.(Bello Wang)