in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Antonio Guterres ya jinjinawa ci gaban da kasashen Afirka suka cimma a fannin hadin gwiwa domin samar da ci gaba
2017-02-02 12:37:39 cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bayyana irin ci gaba da kasashen Afirka suka cimma, a yunkurin su na hada gwiwa domin cimma nasarorin bunkasa nahiyar.

Yayin cikakken taron sa da manema labarai a karon farko jiya Laraba tun bayan da ya kama aiki, Mr. Guterres ya ce nasarorin da nahiyar Afirka ta cimma babban abun a yaba ne, kuma ga alama hakan na iya taimakawa wajen cimma nasarar wanzar da ci gaban nahiyar, da inganta tsaro, da zaman lafiya mai dorewa. Sai dai kuma ya nuna damuwa game da yiwuwar aukuwar laifuka masu alaka da kisan kiyashi a Sudan ta Kudu.

Babban magatakardar MDDr wanda a baya ya rike mukamin firaministan Portugal, da mukamin shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, ya nuna yabo ga hadin gwiwa da aka yi kan batun sauyin gwamnati a kasar Gambiya, tare da yi tsokaci game da halin da ake ciki a gabas ta tsaki, da matsalar kwararar 'yan gudun hijira.

Har wa yau ya yi tsokaci game da kin amincewar sa da batun hana 'yan gudun hijira shiga Amurka.

Game da taron birnin Astanan kasar Kazakhstan da aka gudanar don gane da rikicin siyasar kasar Syria kuwa, Mr. Guterres ya ce MDD ta shiga an dama da ita, a zaman da kasashen Iran, da Turkiyya da Rasha suka jagoranta, matakin da ya share fagen cimma nasarar da ake fata, a sabon zaman shawarwari da za a gudanar a birnin Geneva, nan gaba cikin wannan wata don gane da kasar ta Syria. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China