in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kula da harkokin mata ta MDD ta yi kira da karfafa tattalin arzikin matan Nahiyar Afrika.
2017-01-27 12:56:27 cri
Hukumar kula da harkokin mata ta MDD ta yi kira da samar da dabaru da manufofi da za su taimakawa nahiyar Afrika tabbatar da habaka tattalin arzikin mata a wannan zamani.

An yi wannan kiran ne jiya Alhamis, yayin wani taron tuntuba na 61 kan harkokin mata a nahiyar Afrika.

Taken taron da aka gudanar a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia shi ne 'habaka tattalin arzikin mata a wannan zamani'.

A jawabinta, babbar daraktar hukumar ta MDD Phumzile Mlambo-Ngcuka, ta ce yanayin aiki a yanzu ya tanadarwa mata manya da kanana, har ma da wadanda suka rasa matsugunansu damarmaki da kalubale da dama.

Hukumar ta MDD ta ce banbancin da ake nunawa mata wajen daukar aiki na dakile musu samun ci gaba, tana mai cewa matsalar na kaiwa ga asarar kimanin dala casa'in da biyar duk shekara tun daga 2010.

Hukumar ta kuma jadadda bukatar samar da hanyoyin da za su tanadarwa mata damarmaki a matsayin wadanda za su zama jagororin tabbatar da sauyi a nahiyar, tare da janye shingen da ke hana su shiga a dama da su cikin harkokin yau da kullum. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China