in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga shugabannin kasashen Afrika su magance matsalar safarar haramtattun kudade
2017-01-28 12:44:05 cri
A jiya Jumma'a, wasu kungiyoyin kishin al'umma sun yi kira ga shugabannin kasashen Afrika, su kara kaimi wajen yaki da safarar haramtattun kudade daga kasa zuwa kasa, al'amarin da suka bayyana a matsayin mai muhimmanci wajen ciyar da nahiyar gaba.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, kungiyoyin sun ce safarar haramtattun kudade na janyo asarar sama da dala biliyan saba'in ga nahiyar, suna masu bayyana shi a matsayin babbar matsalar da nahiyar ke fuskanta a yanzu.

Kungiyoyin da suka bada shawarari da za su taimakawa kasashen yaki da wannan matsala, sun bukaci shugabanni su zage damtse wajen magance matsalar.

Cikin shawarwarin da aka gabatar hadda daukar matakai ta hanyar hadin gwiwar hukumomi daban-daban, domin yaki da safarar haramtattun kudade, da tattara bayanai game da shaidar mallakar kamfanoni da sauran bayanai masu alaka da biyan haraji.

A cewar shugaban shirin yaki da safarar haramtattun kudade na duniya, Raymond Baker, kungiyoyin sun ba da shawarar kasashe su yi amfani da tsarin nan na samun kudi da kansu ta yadda za su kashawa al'ummominsu, da nufin cimma muradun ci gaba masu dorewa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China