in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zambia ya bayyana cancantarsa ta tsayawa takara a zaben 2021
2017-01-06 13:23:23 cri
A jiya Alhamis ne Shugaban kasar Zambia Edga Lugun ya ce, ya cancanci tsayawa takara a zaben 2021, yana mai kalubalantar wadanda da ke kira da samar da sauyin shugabanci.

Rikici ya barke a Jam'iyyar PF mai mulkin kasar, inda wasu jagororinta ke kira da a gudanar da zabe domin samun sabbin shugabanni.

Da yake jawabi ga 'ya'yan Jam'iyyar a garin Luanshya dake lardin Copperbelt, Edgar Lugu ya ce kundin tsarin jam'iyyar da ya yi nazari, ya fayyace damar da yake da ita ta tsayawa takara a shekarar 2021

Da yake mai da martani game da korafin da 'yan Jam'iyyar suka yi cewa, an ba wadanda suka sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta MMD mukamai maimakon 'yan asalin jam'iyya mai mulki, Edgar Lugu ya yi kira gare su su yi maraba da sababbin mambobi, domin jam'iyyar na bukatar karin magoya baya gabannin zaben 2021.

Ya ce mutanen dake adawa da sake tsayarwasa takara su je su duba kundin tsarin jam'iyyar domin ganin abun da doka ta tanada.

Ya kuma kalubalanci jagororin jam'iyyar dake kawu rarrabuwar kawuna da su fice, yana mai cewa, muradinsa shi ne tabbatar da jam'iyyar matsayin tsintsiya madaurinki daya.

Edgar Lugu ya zama shugaban kasa a karon farko a shekarar 2015, bayan an gudanar da zaben sanadiyyar mutuwar shugaban kasar na wancan lokaci Micheal Sata. Sannan, ya sake lashe zaben da aka yi a ranar 11 ga watan Augustan 2016. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China