in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fashewar tagawayen bama-bamai a kusa da sansanin sojin kungiyar Tarayyar Afrika dake Somalia, ya yi sanadin mutuwar mutane biyu
2017-01-03 09:49:50 cri
Harin tagwayen bama-bamai da kungiyar Al Shaabab ta kai jiya Litinin, kusa da sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afrika AMISOM da wani babban Otel a Mogadishu Babban birnin kasar Somalia, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.

Wani Dan Sanda Mohammad Jama dake wurin da al'amarin ya auku, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin cewa, bam na farko ya fashe ne a wani shingen binciken sojoji, wanda ke kusa da hanyar shiga sansanin Halane, dake kusa da filin jirgin saman birnin.

A kusa da sansanin na Halane kuma, akwai wani babban Otel da jami'an diflomasiyya da manyan Jami'an gwamnati ke zuwa, dan ko a 2016, an yi wani taron yini guda na shugababnninn kasashen yankin Afrika ta gabas a Otel din.

Kakakin rundunar AMISOM Joe Kibet ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, harin kunar bakin wake aka kai shingen binciken a cikin wata mota, yayin da daga bisani, dakarun tarayyar Afrika suka kai farmaki kan wata mota mai dauke da bam da ya doshi sansanin da kimanin nisan mita 200.

Ya kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, babu wani sojan AMISOM, sai dai fararen hula.

Sai dai wani shaidar gani da ido ya ce tagawayen bama-baman sun yi sanadin mutuwar a kalla mutane hudu

Tuni dai kungiyar Al Shabaabb wadda ta shafe shekaru tana yaki da gwamnatin kasar ta dauki nauyin kai hare-haren. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China