in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama wasu da ake zargin 'yan kungiyar Al-shabaab ne a babban birnin kasar Somalia
2017-01-04 10:42:51 cri

Jiya Talata, jami'an tsaro a Somalia sun cafke wasu mutane biyu da ake zargin 'ya'yan kungiyar Al-Shabaab ne, a wani aiki da suke na farautar wadanda ke da hannu a kisan wani sojan gwamnatin kasar.

Kwamishinan 'yan sandan yankin Benadir, Bishar Abshir Gedi, ya ce ana zargin mutanen biyu na da hannu a kisan wani jami'in soji da aka yi a lardin Yakshid ranar Litinin da dare.

Mutuwar sojan ta zo ne sa'o'i, bayan bayan mayakan Al-Shabaab sun kai tagwayen harin Bam a birnin Mogadishu ranar Litinin, inda suka yi ikirarin hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da talatin.

Sai dai har yanzu, ba a san takamaimai adadin mutanen da hare-haren ya rutsa da su ba. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China