in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU ta tura tawagar kwararru don tallafawa aikin gudanar da babban zabe a kasar Somalia
2016-09-25 12:48:02 cri
Kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU ya sanar a birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar Somalia, a ranar Asabar, cewa kungiyar AU ta riga ta tura wata tawagar kwararru zuwa kasar Somalia, wadda za ta ba da tallafi ga aikin gudanar da babban zabe a kasar, musamman ma a fannin fasahar gudanar zabe.

Cikin sanarwar, an yi bayani kan ayyukan da tawagar kwararrun za ta aiwatar, wadanda suka kunshi sa ido kan yadda ake gudanar da zaben da ba na kai tsaye ba a Somalia a shekarar 2016, gami da rike shi yadda ya kamata. Haka kuma za su share fage ga wani shirin siyasa da aka tsara na ganin kowane dan kasar Somaliya ya jefa kuri'arsa guda zuwa shekarar 2020.

Sauran ayyukan da kwararrun kungiyar AU za su gudanar sun hada da hadin gwiwa tare da MDD, da kungiyar tarayyar kasashen Turai EU, da kungiyar kasashen Larabawa, don tabbatar da gudanar babban zaben a kasar Somalia lami lafiya, ba tare da gamuwa da matsala ba. Sa'an nan, an ce tawagar kwararrun za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 5 ga watan Nuwamban bana.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China