Khamenei ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Amurka ta yanzu ta gudanar da wasu ayyukan da suka sabawa yarjejeniyar makamashin nukiliya, ciki har da tsawaita wa'adin takunkumin da aka sakawa kasar Iran da shekaru 10. Idan aka aiwatar da kudurin, babu shakka wannan aiki ya sabawa yarjejeniyar makamashin nukiliya, kuma kasar Iran za ta mayar da martani.
A ranar 15 ga wannan wata, majalisar wakilan kasar Amurka ta amince da tsawaita wa'adin takunkumin da aka sakawa kasar Iran da shekaru 10 ta hanyar jefa kuri'u. A mahawarar da aka yi game da wannan batu, membobin majalisar wakilan Amurkar 419 ne suka jefa kuri'ar amincewa, daya ne tak ya ki amincewa. Yanzu haka an mika wannan kuduri ga majalisar dattijai ta kasar. (Zainab)