Haysom yayi wannan kiran ne bayan wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir a birnin Khartoum.
Yace kasashen duniya suna kokarin maido da zaman lafiya, da kuma karin fahimtar juna tsakanin kasashen Sudan da makwabciyarta Sudan ta kudu, don lalibo hanyoyin da zasu samar da damammaki na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin kasashen biyu.
Haysom, yace ya kamata a maido da cikakken zaman lafiya tsakanin kasashen ta hanyar yin tattaunawa tsakanin kasashen biyu.
A yayin ganawar tasa da al-Bashir, Haysom yace, sun sake bibiyar halin da ake ciki game da irin rawar da Sudan ke takawa wajen ingiza zaman lafiya a Sudan ta kudu, kasancewa kasar ta Sudan babbar mamba ce a kungiyar raya cigaban kasashen gabashin Afrika IGAD.