in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shawarwari tsakanin ministocin harkokin waje na Sin da Sudan
2016-10-28 19:54:46 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Sudan Ibrahim Ghandour a juma'ar nan a birnin Beijing.

A yayin ganawar ta su, Mr. Wang ya bayyana cewa, kasarsa na jinjinawa goyon bayan kasar Sudan, game da batutuwan da suka shafi babbar moriyar kasar Sin, da batutuwan da Sin ke matukar damuwa a kan su cikin tsawon lokaci. Wang ya kara da cewa, kasar Sin na ci gaba da goyon bayan kokarin da bangaren Sudan ke yi a fannonin kiyaye mulkin kai, da 'yancin kai, da kuma tabbatar da cikakken yankin kasa. Tana kuma fatan ci gaba da nuna amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare, da karfafa hadin kai irin na samun moriyar juna tsakanin sassan biyu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China