Bataliyar dai tana kunshe ne da dakaru 700, kuma za su tashi zuwa kasar Sudan ta kudu ne cikin rukunoni 6, inda za su gudanar da ayyukan ba da kariya ga fararen hula da ma'aikatan agajin jin kai na MDD da kuma sintiri da tsaro.
Kafin su tashi, sai da suka kwashe watanni uku suna samun horo a fannoni 22, kuma dukkan dakarun sun ci jarrabawar da aka yi musu, kuma suna da kwarewa a fannin samar da tsaro.(Lubabatu)