in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara gasar cin kofin nahiyar Afirka a kasar Gabon
2017-01-18 15:44:45 cri

A ranar Asabar da ta gabata ne aka bude babbar gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin Afirka a kasar Gabon, inda a wasan farko da aka buga, Gabon, dake matsayin mai masaukin baki a gasar ta bana, ta yi kunnen doki da Guinea Bissau da ci 1 da 1.

Shugaban kasar Ali Bongo shi ne ya sanar da bude gasar a hukunce, a birnin Libreville fadar mulkin kasar ta Gabon. Wannnan dai gasa ita ce mafi muhimmanci a fannin wasan kwallon kafa a nahiyar Afirka. Bayan kaddamar da gasar ne kuma aka fara buga wasa na farko tsakanin Gabon da Guinea Bissau.

Kungiyoyin 2 ba su samu cin kwallaye ba, har sai bayan mintuna 52 da fara wasan, inda kyaftin din kungiyar Gabon, kuma mai rike da kambin dan wasan mafi kwarewa a Afirka na shekarar 2015 Pierre Aubameyang, ya ci kwallon farko a wasan. Sai dai a nasu bangare, 'yan wasan kungiyar Guinea Bissau sun yi kokarin kare gidansu tare da jiran dama. Zuwa minti na 89, Juary Soares na Guinea Bissau ya samu damar buga kwallo da ka, kuma kwallon ya shiga ragar Gabon. Haka aka tashi da ci 1 da 1 a wasan na farko da aka buga a gasar AFCON ta wannan shekara.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China