Cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a Nairobi, Kenyatta, ya ce ta hanyar huldar kasuwanci ne al'ummomin kasashen dake yankin kudu maso kudanci za su ci moriya.
Shugaban na Kenya ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ba da dukkannin goyon bayan da ake bukata domin bunkasa dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen yankunan kudu maso kudanci.
Tawagar wakilan kasashen ta ziyarci kasar Kenya ne a karon farko, domin halartar taron koli na huldar kasuwanci tsakanin kasashen Latin Amurka da na Caribbean da kuma Afrika wanda ke gudana a birnin Nairobi. (Ahmad Fagam)