in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sako wata 'yar Kenya da 'yan fashin teku suka sace a shekarar 2014
2016-10-31 10:39:32 cri
Dakarun musammun na yankin Galmudug dake tsakiyar kasar Somaliya sun kwato a ranar Asabar wata 'yar Kenya da 'yan fashin tekun Somaliya suka sace a shekarar 2014, a cewar wasu majiyoyi masu tushe a ranar Lahadi.

Loise Njoki, tana hannun hukumomin wannan yanki mai cin gashin kansa kafin a mayar da ita zuwa Kenya.

Andrew Mwangura, jami'in gudanarwa na ayyukan teku na gabashin Afrika, ya bayyana cewa aikin ceton sojojin musammun ya gudana cikin nasara.

Ana binciken lafiyar jikinta a halinzu kuma za a mayar Kenya domin saduwa iyalenta, in ji mista Mwangura.

An sace Loise Njoki tare da James Kuria a yayin da suke kokarin kai magunguna a Mogadiscio. Jami'an tsaron Somaliya sun ceto mista Kuria a cikin watan Febrairun shekarar 2015.

Saidai kuma har yanzu ba a da labarin wasu 'yan kasar Kenya biyu da mayakan na Somaliya suka sace a shekarar 2014, George Macharia Mburu da George Macharia Njoki. Mutanen biyu suna wa wani kamfanin gine gine (BTP) na Kenya dake Mogadiscio aiki a lokacin da aka kama su a yankin Habargidir na Somaliland dake arewaci.

Haka kuma wani na daban dan Kenya, Patrick Amukhuna, har yanzu yana hannun 'yan fashin teku tun lokacin da suka sace shi a shekarar 2008. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China