in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Kenya ya ja hankalin hukumar yaki da cin hanci
2016-10-19 10:48:48 cri
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya ja hankalin hukumar dake yaki da cin hanci da karbar rashawa a kasar sa, da ta kara kwazo wajen dakile zamba da cin amanar kasa, matsalolin da ke ci gaba da zama tarnaki ga ci gaban kasar.

Shugaba Kenyatta wanda ya ce gwamnatin sa ce ta daya waje yaki da cin hanci da rashawa, idan aka kwatanta da sauran gwamnatocin da suka gabata, tun samun 'yancin kai ya zuwa wannan lokaci, ya kara da cewa gwamnatin ta gurfanar da manyan jami'an hukuma da dama, wadanda suka aikata wadannan laifuka, a gaban kuliya.

Shugaban na Kenya wanda ke wannan kalamai yayin wani taron karawa juna sani a birnin Nairobi, ya ce matsalar cin hanci da rashawa, na cikin abubuwan da ke ci masa tuwo a kwarya. Daga nan sai shugaba Kenyatta ya bukaci al'ummar kasar da su raba cin hanci da batun siyasa, yana mai cewa akwai bukatar kotuna su kara azama, wajen kammala shari'un da ke da nasaba da cin hanci da aikata almundahana.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China