Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara zage damtse, wajen yaki da laifuka masu alaka da cin hanci ko karbar rashawa, yana mai cewa ya zama wajibi a fadada wannan aiki, tare da aiwatar da daukacin manufofin JKS cikin tsari, kwarewa da nagarta.
Shugaba Xi wanda kuma shi ne babban sakatare na kwamitin tsakiyar JKS, kana shugaban babbar hukumar soji ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne yayin taro na 7, na hukumar kula da da'a da sanya idanu ta 18 ta kwamitin tsakiyar JKS. (Saminu Hassan)