in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 3 sun jikkata a sakamakon fashewar abubuwa a filin jirgin saman Shanghai
2016-06-12 17:58:51 cri
Hukumomi sun tabbatar da cewar kimanin fasinjoji 3 ne suka jikkata a sakamakon fashewar wasu abubuwa a filin jirgin saman Pudong na birnin Shanghai.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 2:20 na yammacin wannan rana a kusa da inda ake tantance fasinjoji a sashe na 2 na filin jirgin saman.

Hukumomin kula da zirga zirgar jiragen saman na Shanghai sun tabbatar da cewar wasu ababen fashewa da aka hada da hannu ne suka fashe.

Sai dai tuni aka garzaya da wadanda suka jikkatan zuwa asibiti, sannan ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China