in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na alhinin rasuwar Keshi
2016-06-09 13:13:46 cri
Alummar Najeriya daga dukkan sassan kasar na cigaba da nuna juyayi dangane da rasuwar tsohon kyafti kuma mai horas da 'yan wasan kulub din Super Eagles na kasar Stephen Keshi.

Keshi ya rasu ne cikin daren jiya Laraba sakamakon cutar bugun zuciya da kuma ciwon kafofi.

Marigayin shi ne mutumin da ya fi jimawa a matsayin kaftin din kungiyar wasan Najeriyar, kuma a lokacinsa ne kulub din kasar ya samu nasarar lashe lambobin yabo na cin kofin kasashen Afrika a shekarun 1994 da 2013.

A wata sanarwa shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya bayyana Keshi a matsayin gwarzon dan wasan kwallon kafa kuma koci

Shi ma mataimakin shugaban Najeriyar Yemi Osinbajo ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, wanda ya rasu yana da shekaru 54 a duniya.

Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, da ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, da 'yan siyasa da dama sun bayyana alhinunsu game da rasuwar gwarzon dan wasan kana kocin kulon din kafan na Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China