Hukumar kula da al'amurran wasannin kwallon kafa ta Najeriya ta sanar da karbi takardar barin aiki daga tsohon kocin kungiyar wasan kwallon kafar kasar Super Eagles Sunday Oliseh.
Shi dai mista Oliseh, ya ayyana yin murabus daga shugabancin kungiyar wasan ta Super Eagles ne a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ya bayyana cewar, ya dauki wannan mataki ne sakamakon abin da ya kira da rashin cika ka'idojin yarjejeniyar da aka kulla tsakaninsa da hukumar wasannin kasar, ciki har da rashin biyan sa kudaden albashi, inda ya dora alhakin hakan kan hukumar kula da wasan kwallon kafan kasar NFF.
To sai dai hukumar ta NFF bayan ta amshi takardar yin murabus din ta Oliseh, ta musanta zargin, ta ce, babu wani rashin jituwa a tsakaninta da tsohon mai horas da 'yan wasan na Super Eagles.
Kafin yin murabus din, Najeriya ta sha alwashin Oliseh ne zai jagoranci kungiyar wasan ta Super Eagles a gasar share fagen cin kofin kasashen Afrika da za'a gudanar a wata mai zuwa.
NFF ta maye gurbin Oliseh da tsohon 'dan wasa Samson Siasia a matsayin kocin Super Eagles na riko.(Ahmad Fagam)