in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon kociyan Najeriya Shaibu ya rasu
2016-06-12 12:00:27 cri

Tsohon kociyan kungiyar wasan kwallon kafan Najeriya Super Eagles Amodu Shaibu ya rasu, yana da shekaru 58 a duniya.

Hukumar kwallon kafa ta kasar (NFF) ta tabbatar da mutuwarsa a jiya Asabar.

Mutuwar Amodu ta zo ne kwanaki 3 bayan rasuwar tsohon kefti kuma kociyan kungiyar Super Eagles Stephen Keshi, wanda ya rasu, yana da shekaru 54, a birnin Benin dake shiyyar kudancin Najeriya a ranar Larabar da ta gabata.

Hukumar NFF ta ce, marigayi Shaibu, wanda shi ne daraktan tsare tsare na hukumar kwallon kafan kasar, ya koka game da matsalar ciwon kirji dake damun sa gabanin mutuwarsa a daren Juma'ar da ta gabata.

Marigayin 'dan asalin jihar Edo dake shiyyar kudu maso gabashin Najeriyar ya rike mukamin kociyan babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar har sau hudu a lokuta dabam dabam.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China