in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce mutane 290 sun hallaka a yunkurun juyin mulkin kasar
2016-07-18 09:28:04 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce a kalla mutane sama da 290 ne aka kashe a yunkurin juyin mulkin kasar da bai yi nasara ba.

Daga cikin wadanda suka mutu, akwai fararen hula 190, da kuma wadanda suka shirya juyin mulkin su 100, sanarwar ta kara da cewar, sama da mutane 1,400 ne suka samu raunuka a lokacin yunkurin juyin mulkin na daren jumma'a, wanda aka dakile shi a safiyar Asabar da ta gabata.

Ya zuwa yanzu, an cafke mutane sama da dubu 6 wadanda ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin.

Sanarwar ta kara da cewar ana zargin malamin addinin musulunci na kasar Fethullah Gulen ne ya shirya juyin mulkin.

Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyyar ta ce za ta ci gaba da zakulo dukkanin wadanda ke da alaka da kungiyoyin ta'addanci a kasar, da shugabansu Fethullah da sauran dukkan masu ruwa da tsaki. Yunkurin juyin mulkin kasar ya kasance wata babbar barazana wanda ake danganta shi da Fethullah Gulen, wanda a halin yanzu yake gudun hijira a Amurka. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China