Bayan wasu 'yan sa'o'in da wasu sojoji suka nemi kifar da gwamnatinsa, shugaba Erdogan wanda yake hutu a garin Marmaris dake bakin teku a kudu maso yammacin kasar ya dawo birnin Istanbul, tare da samun kyaukyan tarbo a filin jiragen sama.
A yayin wani taron manema labaru da aka shirya jim kadan, Mr. Erdogan ya zargi lamarin yunkurin juyin mulki cewa, "lamari ne na namen ta da zaune tsaye" da "cin amana". Ya ce, zai kawar da dukkan wadanda suka yi wannan yunkurin juyin mulki daga rundunar sojan kasar gaba daya. Sannan, shugaba Erdogan ya zargi Fetura Gulen, wani dan Turkiyya wanda ke gudun hijira a kasar Amurka da jagoranta wannan makarkashiya, kuma shugaba Erdogan ya kira ga jama'ar kasar da su fito kan tituna su yi zanga-zanga domin nuna goyon bayan gwamnati mai ci. Bugu da kari, ya nemi sojoji kada su bude wuta kan 'yan uwansu da kasarsu ta asili.
Bisa labari daban da aka bayar, an ce, firayin ministan kasar Turkiyya Bina Le Yıldırım ya nemi 'yan majalisar dokokin kasar da su shirya wani taron gaggawa domin tinkarar hargitsin da ake fama da shi a kasar.
Game da halin ta da zaune tsaye da ake ciki a kasar Turkiyya, Mr. Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin na mai da hankalinta sosai kan halin da ake ciki a kasar Turkiyya, tana fatan za a iya maido da oda da kwanciyar hankali a kasar Turkiyya cikin sauri. (Sanusi Chen)