in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira da a warware batun Syria ta hanyar yin shawarwari
2016-12-14 13:23:43 cri
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya yi kira da a sake komawa teburin shawarwarin warware batun Syria, da nufin kawo karshen ricikin kasar.

Wu ya bayyana hakan ne a jiya Talata 13 ga watan nan, a yayin da yake jawabi a taron gaggawa da kwamitin sulhun MDD ya shirya a wannan rana, inda aka saurari rahoton da Ban Ki-Moon ya gabatar don gane da yanayin da ake ciki a birnin Aleppo dake arewacin Syria.

Mr. Wu ya kara da cewa, kasar Sin na fatan yin kokari tare da sauran kasashen duniya, don inganta shirin warware batun kasar ta Syria ba tare da wani bata lokaci ba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China