in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ta amsa tambaya game da Sao Tome and Principe ta yanke huldar diplomasiyya da yankin Taiwan
2016-12-21 10:14:04 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta amsa tambayoyi game da kasar Sao Tome and Principe ta yanke dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da yankin Taiwan a yau Laraba.

Hua ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sao Tome and Principe ta bayar da sanarwa a jiya Talata cewa, ta tsai da kudurin yanke dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da yankin Taiwan, Sin ta nuna yabo ga kudurin, da yin maraba da matakin da kasar ta dauka na bin ka'idar Sin daya tak.

Hua ta kara da cewa, a halin yanzu, tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak ya dace da yanayin kasa da kasa da burin jama'a. Sin tana son raya dangantakar hadin gwiwa da sada zumunta a tsakaninta da sauran kasashen duniya bisa tushen ka'idoji biyar na zaman tare cikin lumana da ka'idar Sin daya tak. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China