in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya amsa tambayoyi game da wayar tarho da shugaban kasar Amurka ya bugawa jagorar yankin Taiwan
2016-12-04 13:56:01 cri
Game da wayar tarho da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bugawa jagorar yankin Taiwan Tsai Ing-wen, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, Sin ta riga ta tuntubi kasar Amurka game da wannan batu.

Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, yankin Taiwan wani kashi daya ne na kasar Sin. Gwamnatin kasar Sin halaliyyar gwamnati ce dake wakilci kasar Sin baki daya, wadda kuma kasa da kasa sun amince da ita.

Ka'idar Sin daya tak tushen siyasa ne yayin da ake raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, Sin ta kalubalanci hukumomin kasar Amurka da abin ya shafa da su bi manufar Sin daya tak, da cika alkawarin ka'idojin hadaddiyar sanarwa na Sin da Amurka guda uku, da warware batun yankin Taiwan yadda ya kamata don magance matsalolin dake kawo illa ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China