in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu tace sanyawa kasar takunkumin sayo makamai ba zai magance rikicin kasar ba
2016-11-19 12:27:53 cri
Gwamnatin Sudan ta kudu ta fada a jiya Juma'a cewa, matakin da Amurka ta dauka na azawa kasar takunkumin kin sayar mata makamai ba zai iya kawo karshen tashin hankali a kasar ba.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Mawen Makol Arik, ya fada cewa barazanar kin sayarwa kasar makamai zai iya kara dagula al'amurra, kuma matakin zai iya wargaza shirin yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a bara tsakanin bangarorin kasar da basa ga maciji da juna.

Arik ya ce, babu wani dalili da zai sa a haramtawa kasar sayen makamai, kasancewar ana cigaba da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar.

Sudan ta kudu ta tsunduma cikin yakin bassa ne tun a watan Disambar shekarar 2013, bayan da shugaban kasar Salva Kiir ya zargi hambararren mataimakinsa Riek Machar, da yunkurin yi masa juyin mulki. Sai dai mista Machar din ya sha musanta zargin da ake yi masa, lamarin da ya sa daga bisani ya kafa rundunar mayaka dake karkashin ikonsa.

An kulla yarjejeniyar zaman lafiyar ne tsakanin Kiir da Machar a watan Augastan bara karkashin MDD, da nufin samar da gwamnatin hadin kan kasar, to sai dai yunkurin bai samu nasara ba, sakamakon sabon fadan da ya rincabe a kasar a farkon watan Yulin wannan shekara.

Arik, ya ce, gwamantin Sudan ta kudun bata da niyyar wargaza shirin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar da aka amince da ita a watan Augasta, kana ta bukaci kasashen duniya da su sa baki wajen daukar duk wasu matakai da za su kawo karshen rikicin kasar ta hanyar tattaunawar sulhu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China