Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana a jiya Litinin cewa, yana da kyakkyawan fata cewa, halin matsin tattalin arziki da kasar ta shiga zai zo karshe a shekarar 2017 mai kamawa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja, fadar mulkin kasar, a lokacin da ya jagoranci bude taron bita wanda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta shiryawa jami'an ofisoshin jakadancin kasar.
Shugaba Buhari ya bayyana kwarin gwiwa cewa, dalilan da suka haddasa matsin tattalin arzikin kasar, za'a dakile su a shekarar mai kamawa.
A cewarsa, halin komadar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi ya sanya kasar yin wasu sauye sauye game da manufofinta na hulda da kasashen ketare.
Ya bukaci jakadun Najeriyar a kasashen waje, da su aiwatar da kyawawan manufofi wadanda za su daga kimar kasar a kasashen waje, kana su ba da gudunmowarsu wajen ci gaban Najeriya a yayin mu'amala da kasashen duniya.(Ahmad Fagam)