A jiya ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sallami manyan hafsoshin rundunonin sojojin kasar, inda ya maye gurbinsu da sabbi, a wani mataki na yiwa rundunonin sojojin kasar garambawul a yakin da suke da mayakan Boko Haram.
Wata sanarwa mai dauke da sanya hannun kakakin shugaban Femi Adesina ta ce, shugaba Buhari ya kuma amince da nadin manjo janar Abayomi Gabriel Olonishakin a matsayin babban hafsan tsaron kasar sai kuma manjo janar Tukur Yusuf Buratai wanda aka nada a matsayin babban hafsan sojojin kasa.
Sauran sun hada da Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin babban hafsan mayakan ruwa sai Air Vice Marshal Sadique Abubakar wanda shugaban ya nada a matsayin babban hafsan sojojin saman kasar. Yayin da shugaba Buhari ya amince da nadin manjo janar Babagana Monguno mai ritaya a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.
Sanarwar ta ce, dukkan wadanda aka nadan za su yi aiki ne na wucin gadi har zuwa lokacin da majalisar dattawan kasar za ta amince da nadin nasu.
Masu sharhi kan al'amuran tsaro a kasar na ganin cewa, za a damkawa sabbin manyan hafsoshin da aka nadan alhakin kawar da mayakan na Boko Haram daga ko wane lungu da sako na kasar.(Ibrahim)