Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya umarci mai ba shi shawara kan harkokin tsaro da ya kafa wani kwamiti mai mutane 13 domin ya binciki yadda aka sayo makaman da sojojin kasar ke amfani da su tun daga shekarar 2007 zuwa wannan lokaci, a wani mataki da shugaban kasar ya dauka na ganin an kakkabe cin hanci da rashawa a kasar.
Wata sanarwa da kakakin fadar shugaban kasar Femi Adesina ya rabawa manema labarai ta ce, binciken ya biyo bayan kalubalen da dakarun kasar suke fuskanta ne a yakin da suke yi da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya shafi kwazon dakarun.
Sanarwar ta bayyana cewa, shugaba Buharin ya umarci kwamitin da ya binciko dukkan matsalolin da aka fuskanta da irin cuwa-cuwar da aka tafba wajen sayo makaman, kana ya gabatar da shawarwarin da suka dace kan matakan da za a dauka wajen sayo makaman a nan gaba.
Ana zargin gwamnatocin kasar da suka gabata ne da yin cuwa-cuwa wajen sayo makaman wadanda daga karshe ake karewa da sayo makaman da ba su da inganci (Ibrahim)