Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nuna juyayi tare da yin Allah wadai da harin ta'addacin da aka kai kan fararen hula a birnin Paris na kasar Faransa wanda ake zargin 'yan ta'adda da kaddamarwa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa daga ofishin sa a Abuja a ranar Lahadin nan, sannan ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda hare-haren suka rutsa da su.
Shugaban na Najeriya, ya bayyana harin a matasyin rashin wayewa, kuma ya saba da tunina irin na masu hankali.
A cewar al'ummar Najeriya na taya Faransa juyayin wanann mummunan al'amari.
Shugaba Buhari, ya yi kira ga sauran kasashen duniya masu kaunar zaman lafiya, da su hada gwiwa domin yakar ayyukan ta'addanci a duniya baki daya.(Ahmed Fagam)