A ranar Laraba ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya rantsar da ministocinsu, kwanaki 165 bayan da ya kama aiki.
Nadin ministocin na Najeriya da ya gudana a fadar shugaban kasar da ke Abuja, babban birnin Najeriya ya kawo karshen rashin sanin tabbas na tsawon watanni 6 ga harkokin tattalin arzikin kasar, lamarin da ya kai ga 'yan kasar na cewa, kusan al'amura sun tsaya cik.
A jawabinsa yayin bikin rantsar da sabuwar majalisar ministocin mai kunshe da tsoffin gwamnoni, 'yan siyasa da kwararru daga sassa daban-daban, shugaba Buhari ya bukace su da su zage damtse don ciyar da kasar gaba.
Kafin nadin ministocin, sai da shugaba Buhari ya sallami manyan sakatarorin tarayyar kasar guda 17, a wani mataki na yiwa harkokin aikin gwamnatin kasar gyaran fuska, inda nan take ya maye gurbinsu da wasu sabbi guda 18. 'Yan Najeriya na masu imanin cewa, mutanen da shugaban ya nada za su kai ga samar da canjin da ake bukata a kasar.
A hirarsa da manema manema labarai, shugaban majalisar dattawan Najeeiya Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana imanin cewa, nada ministocin zai samar da canjin yanayin aikin da ake bukata a kasar.(Ibrahim)