140504murtala.m4a
|
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sanar da cewa, domin tabbatar da cikakken yanayin tsaro da maganin matsalar cunkoso, za'a rufe dukkanin makarantu gami da sassan gwamnati, a yayin taron kolin kasashen Afirka na dandalin tattalin arzikin duniya, wanda za'a yi daga ranar 7 zuwa 9 ga wata a Abuja, fadar gwamnatin kasar.
Taron da za'a shafe tsawon kwanaki uku ana yi, zai samu halartar manyan baki daga kasashen duniya da dama, ciki har da shugabannin kasashen Afirka, da fitattun 'yan kasuwa da sauransu. Firaministan kasar Sin Mista Li Keqiang yana ciki mahalarta taron, zai kuma jagoranci wata babbar tawaga domin halartarsa, inda zai gabatar da wani muhimmin jawabi game da ingiza hadin-gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannoni daban-daban.
Jama'a dai na ganin cewa, umurnin na shugaba Jonathan ba ya rasa nasaba da rashin kwanciyar hankalin da ake fama da shi a wasu sassa na babban birnin tarayya Abuja. Ko da a ranar Alhamis din da ta gabata ma dai sai da wani bom ya fashe a yankin Nyanya dake wajen birnin na Abuja, kusa da wurin da wani bom din ya tashi, kusan makonni ukun da suka gabata, wanda ya hallaka mutane sama da 70, tare da jikkata wasu sama da 100. Yayin da kuma harin ranar Alhamis ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 20, tare da jikkata wasu 85.
A baya dai matsalar harin ta'addanci ta fi addabar arewa maso gabashin Najeriya, amma a halin yanzu an fara ganin bullar hare-haren a babban birnin tarayyar kasar Abuja.