A jiya Lahadi ne aka sanar da kafa sabuwar gwamnati a kasar Lebanon karkashin firayin minista Saad Hariri.
Sakataren majalisar ministocin kasar Fouad Fleifel ne ya sanar da hakan, bayan kammalawar tattaunawar da aka yi a fadar shugaban kasar tsakanin shugaban kasar Michel Aoun da Saad Hariri a gaban shugaban majalisar dokokin kasar Nabih Berri.
Saad Hariri wanda aka bukaci ya kafa majalisar zartarwar wa'adin farko na gwamnatin Michel Aoun, ya fuskanci tarnakin siyasa daban-daban kafin a cimma matsayar da ta kai ga kafa gwamnatin. (Fa'iza)