Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu na M.D.D. ya damu matuka game da rikicin siyasar kasar sakamakon rashin shugaban kasa har na tsawon watanni 21. Ya kara da cewa, wannan ya haifar da babban kalubale a fannonin tsaro, tattalin arziki, zamantakewar al'umma da aikin jin kai na kasar.
Don haka kwamitin sulhu na M.D.D. ya bukaci bangarori daban daban na kasar da su hanzarta ganawar majalisar don ganin an shirya zaben shugaban kasar
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, kwamitin sulhu na M.D.D. ya nuna damuwa sosai game da mummunan tasiri da rikicin Syria ya haifar wa kasar Lebanon. Kwamintin sulhu na M.D.D. ya bukaci bangarori daban daban na Lebanon da su guji tsoma baki cikin rikicin da ake samu a kasar Syria.(Bako)