in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'yan tawaye za su fice daga birnin Aleppon kasar Syria da asubahin ranar Laraba
2016-12-14 09:52:08 cri
DAMASCUS, Dec.13 (Xinhua) – rahoton gidan talabijin na –Arab al-Mayaddeen ya ruwaito cewa, 'yan tawayen za su fice daga birnin Aleppo dake arewacin Syria ne da asubahin ranar Laraba.

Rahoton ya ce, fitar 'yan tawayen ya biyo bayan yarjejeniyar da aka kulla na kyale su, su fice daga yankunan dake karkashin ikonsu a gabashin birnin Aleppo zuwa yammacin birnin.

Za a kwashe Wani adadin 'yan tawayen da ba a bayyana ba daga birnin Aleppo, inda za a bi da su ta hanyar al-Ramuseh zuwa yankin Rashidien, hanya daya kenan da a yanzu ake amfani da ita wajen shiga da fita daga birnin na Aleppo.

Fararaen hulka dai, na da damar ci gaba da zama a yankunansu.

Ana sa ran nan ba da dadewa ba, babban kwamandan rundunar sojin Syria zai bayyana matsayar Syria a hukumance game da al'amarin na Aleppo.(Faeza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China