An ce, bangarorin da rikicin ya shafa sun dakatar da aikin soja a safiyar ranar 14 ga wannan wata, manyan motoci fiye da 10 da gwamnatin kasar Syria suka shirya sun tsaya a wajen yankin Salahuddin dake gabashin birnin Aleppo, da jira dakaru masu adawa su janye daga yankin. Amma ba su janye cikin lokaci ba. An ce bangarorin biyu sun sake fafatawa, suna masu zargin juna da sabawa yarjejeniyar tsagaita bude wutar.
Hukumar sa ido kan tsagaita bude wuta a Syria ta kasar Rasha ta bayyana cewa, dakaru masu adawa da gwamnatin Syria sun yi amfani da damar tsagaita bude wutar wajen tattara karfin su, don kai hari ga sansanin sojojin gwamnatin kasar, daga baya kuma sojojin gwmnatin kasar suka mayar da martani.
Sai dai a nasu bangare dakarun 'yan adawar sun bayyana cewa, sojojin gwamnatin ne suka kai musu hare-hare ta sama da boma-bomai a yankunan su. (Zainab)