in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhang Dejiang ya gana da shugaban kasar Gabon
2016-12-08 21:27:34 cri
A yau Alhamis ne shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya gana da shugaban kasar Gabon Ali-Bongo Ondimba a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing.

Zhang Dejiang ya bayyana cewa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwa tare da majalisar wakilai da ta dattijai ta kasar Gabon ta yadda za a bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Gabon a dukkan fannoni.

A nasa bangare, shugaba Bongo ya yabawa kasar Sin bisa ga goyon bayan da ta ke nunawa ga batun raya Afirka, yana fatan ta wannan ziyara, kasashen biyu za su kara inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya da hadin gwiwa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China