in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Gabon
2016-12-07 20:41:59 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Gabon, Ali Bongo Ondinba, a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, a yau Laraba. Yayin ganawarsu, shugabannin 2 sun yanke shawarar kara yaukaka huldar dake tsakanin Sin da Gabon, da zummar samun ci gaban kasashen 2 tare.

Cikin jawabinsa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, kasar Sin za ta kara tallafawa kokarin Gabon na raya masana'antu, da taimakawa kamfanonin kasar Sin ta yadda za su kara taka rawa a hadin gwiwar bangarorin 2 ta fuskar gina kayayyakin more rayuwar jama'a. Haka kuma ya ce, kamata ya yi, bangarorin 2 su kara musayar ra'ayi kan harkokin duniya, musamman ma a fannonin tinkarar matsalar sauyin yanayi, da samar da zaman lafiya a nahiyar Afirka, ta yadda za a samu damar kare moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa.

A nasa bangaren, shugaba Ali Bongo na kasar Gabon ya ce kasarsa na son kara hada kai tare da kasar ta Sin, bisa manyan shirye-shiryen hadin gwiwa guda 10 da shugaba Xi ya gabatar, wadanda suka shafi huldar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka. Ta haka, a cewar shugaban kasar Gabon, za a taimakawa kokarin zurfafa abokantakar dake tsakanin nahiyar Afirka da kasar ta Sin.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China